Madrid ta gamu da cikas Barca ta ci gaba

Nacho na bakin ciki Real Madrid ta kasa cin wasanta sau biyu a jere

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Nacho na kukan zuci bayan da Real Madrid ta tashi 2-2 da Las Palmas

Sergio Araujo ya farke wa Las Palmas ana gab da tashi daga wasa yayin da Real Madrid ta kasa nasara karo na biyu a jere a gasar La Liga.

Marco Asensio ne ya fara ci wa Real Madrid wadda ta bakunci 'yan Palma a minti na 33, amma Domínguez ya rama minti biyar tsakani.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 67 sai Benzema ya ci wa Real Madrid ta biyu.

Sai dai kuma wannan nasara ta Madrid ba ta yi karko ba, domin ana gab da tashi ne a minti na 85 sai Araujo ya farke kwallon, aka tashi 2-2.

Bayan wasan na mako na shida Real Madrid tana zaman ta daya a tebur da maki 14.

Barcelona wadda tun da farko ta dan dare matsayi na daya bayan da ta lallasa Sporting Gijon 5-0, ita ce ta biyu da maki 13, yayin da Atletico Bilbao wadda ta ci Sevilla 3-1 tana ta uku da maki 12.

A wasan na mako na shida Eibar ta ci Real Sociedad 2-0, ta zama ta shida a tebur da maki 10, yayin da bakin nata suka yi kasa zuwa mataki na 10 da maki 7.