Ebola da Mai Takwasara sun yi canjaras

Dambe
Bayanan hoto,

Abdurrazak Ebola na bin Mai Takwasara kisan dambe daya

Ebola da Mai Takwasara sun tashi canjaras a wasan damben gargajiya da suka yi da safiyar Lahadi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Ebola dan damben Kudu da Mai Takwasa Guramada sai dai suka yi turmi uku suna dambatawa, amma babu wanda ya dafa kasa a tsakaninsu.

Shi ma damben Dan Aliyu Langa-Langa daga Arewa da Yusuf Shagon Shagon Alabo turmi uku suka yi babu kisa, alkalin wasa Tirabula ya raba su.

Sa zare da aka yi tsakanin Dogon Bunza daga Arewa da Aleka daga kudu sun yi gumurzun turmi fiye da uku kafin daga baya suka hakura da dambe tun da babu kisa.

Damben matasa da aka kara tsakanin Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Bahagon Dan Sharif daga Kudu sun biya 'yan kallo sai dai babu wanda yaje kasa a fafatawar.

Mai Takwasara ya sake dambatawa a karo na biyu tsakaninsa da Bahagon Sisco daga Arewa, kuma shi ne wasan karshe da aka tashi babu kisa.