Nigeria na rukunin farko a kwallon rairayi ta Afirka

Rairayi

Asalin hoton, The NFF

Bayanan hoto,

Nigeria ce za ta karbi bukuncin wasannin kwallon rairayi gasa ta biyu da za a yi a jihar Legas

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf, ta raba jadawalin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta kwallon rairayi a ranar Asabar a Masar.

Nigeria mai masaukin baki tana rukunin farko da ya kunshi Masara da Ghana da Cote d'ivoire.

Rukuni na biyu kuwa ya kunshi mai rike da kofin gasar farko Madagascar da Libya da Morocco da Senegal.

Za a fara gasar daga ranar 13 ga zuwa 18 ga watan Disambar 2016 a jihar Legas ta Nigeria.

Kungiyoyi biyun da suka kai wasan karshe za su wakilci Afirka a gasar kwallon rairayi ta duniya da za a yi a Bahamas a 2017.