Na gamsu da yadda Rooney ke taka leda — Mourinho

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Man United tana mataki na shida a kan teburi da maki 12

Jose Mourinho ya ce ya gamsu da wasan Wayne Rooney, kuma dan kwallon yana da muhimmanci a taka rawar da Manchester United ke yi a tamaula.

Mourinho bai sanya Rooney a karawar da Manchester United ta doke Leiucester City da ci 4-1 a ranar Asabar a gasar Premier ba sai da aka kusa tashi daga wasan.

Mourinho ya ce kyaftin din babban dan kwallo ne a wajensa da United da kuma tawagar Ingila.

Rabon da United ta ki sanya Rooney a farkon wasa tun karawa da ta yi a gasar Premier a Kirsimetin bara.