Man City za ta duba raunin da De Bruyne ya ji

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City tana mataki na daya a kan teburin Premier

Manchester City za ta duba raunin da dan wasanta Kevin de Bruyne ya yi a karawar da ta doke Swansea da ci 3-1 a gasar Premier a ranar Asabar.

City ta sauya dan wasan saura minti tara a tashi daga karawar, inda Jesus Navas ya shiga a madadinsa.

Kociyan City, Pep Guardiola, ya ce bai san girman raunin da dan kwallon mai shekara 25 ya yi ba, illa yana jiran sakamakon da likitoci za su sanar.

Manchester City za ta buga wasanta na gaba da Celtic a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Laraba.

City ce ke mataki na daya a kan teburin Premier, bayan da ta lashe wasanni shida da ta yi a gasar, tana kuma da maki 18.