Mun taka rawar gani a wasanmu da Chelsea — Wenger

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Arsenal tana mataki na uku a kan teburin Premier

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce karawar da suka doke Chelsea 3-0 a ranar Asabar, daya ce daga cikin wasannin da suka fi taka rawa a fagen tamaula.

Arsenal ce ta fi taka rawa a kacokan din minti 45 din farko, kuma lokacin ne Alexis Sanchez da Theo Walcott da kuma Mesut Ozil suka ci mata kwallaye.

Wasan shi ne karon farko da Arsenal ta doke Chelsea tun bayan 2011, kuma karawar da zurawa Chelsea kwallaye da dama tun bayan Afirilun 1997.

Wenger ya ce fafatawar da suka yi, wasa ne da suka taka rawar gani da ta kamata kamar yadda suka tsara.

Nasarar da Arsenal ta samu a kan Chelsea ya sa ta koma mataki na uku a kan teburin Premier, inda Man City wadda ke matsayi na daya ta bata tazarar maki takwas.