Zamalek ta kai wasan karshe a kofin zakarun Afirka

Zakaru

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Zamalek za ta kara da Sundowns a wasan karshe a kofin zakarun Afirka na 2016

Zamalek ta Masar ta kai wasan karshe a kofin zakarun Afirka duk da doke ta 5-2 da Wydad Casablanca ta Morocco ta yi a ranar Asabar.

Zamalek ta ci Wydad 4-0 a wasan daf da karshe na farko da suka yi a Alexandria a makon jiya, hakan ne ya sa ta kai wasan karshe da ci 6-5.

Rabon da Zamalek ta lashe kofin zakarun Afirka tun shekara 14 da suka wuce, za kuma ta fafata ne da Mamelodi Sundowns ta Afirka ta kudu.

Karawa biyu da kungiyoyin za su yi a wasan karshe, Sundowns ce za ta fara karbar bakuncin wasan farko ranar 14 ga watan Oktoba, sannan a yi wasa na biyu a Zamalek mako biyu tsakani.

Sundowns da Zamalek sun kara a wasannin cikin rukuni a bana, kuma Sundowns ce ta yi nasara a dukkan fafatawar.

Duk kungiyar da ta samu nasara za ta wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya ta zakarun nahiyoyi da za a yi a Japan a cikin watan Disamba.