Rangers na daf da lashe kofin Firimiyar Nigeria

Nigeria

Asalin hoton, Twitter NPFL

Bayanan hoto,

Rabon da Enugu Rangers ta lashe kofin Firimiyar Nigeria tun a shekarar 1984

Enugu Rangers na daf da daukar kofin Firimiyar Nigeria, bayan da ta doke Ikorodu United a Legas da ci 2-1 a wasan mako na 37 a ranar Lahadi.

Rangers ta ci kwallon farko ta hannun Obinna Nwobodo, sai Chisom Egbuchulam ya kara ta biyu kafin a je hutu, yayin da Ikorodu ta zare kwallo daya ta hannun Paul Duke daf da za a tashi daga karawar.

Da wannan sakamakon Rangers tana nan a matakinta na daya a kan teburin gasar da maki 60, kuma saura wasa daya ya rage a kammala gasar bana.

Rivers United wadda ke da maki 57 a matsayi na biyu ta tashi wasa canjaras babu ci tsakaninta da Abia Warriors.

Rabon da Enugu Rangers ta lashe kofin Firimiyar Nigeria tun a shekarar 1984, amma tana da shi guda shida da ta dauka a shekarar 1974 da 1975 da 1977 da 1981 da 1982 da kuma 1984.

A ranar Lahadi ake sa zan buga wasannin karshe na gasar bana, inda za a bai wa zakara kofi da kuma kungiyoyi hudun da za su yi bankwana da gasar da za a yi ta badi.

Ga wasu daga sakamakon wasannin da aka yi.

  • Nasarawa 2-2 Akwa
  • Sunshine 1-0 Wolves
  • Heartland 1-0 Pillars
  • Tornaoes 3-1 MFM
  • Rivers Utd 0-0 Abia Warriors
  • Ifeanyiubah 1-0 Enyimba