Bahagon Sani zai dambata da Shagon Audu Tunga

Bahagon Sanin Kurna dan wasan Arsewa ya kai zagayen gaba ne
Bayanan hoto,

Bahagon Sanin Kurna zai dambata da Shagon Audu Tunga a wasan daf da karshe a gasar ta damben

Bahagon Sanin Kurna zai dambata da Shagon Audu Tunga a wasan daf da karshe a gasar damben mota a ranar Asabar a filin wasa na Ado Bayero Square da ke jihar Kano.

Bahagon Sanin Kurna dan wasan Arsewa ya kai zagayen gaba ne, bayan da ya samu nasara a kan Shagon Dan Sama'ila dan damben Kudu.

'Yan damben sai da suka yi turmi uku babu kisa a tsakaninsu, amma a lokacin da suke dambatawa a turmin karshe Shagoon Dan Sama'ila ya fita daga cikin da'ira, dalilin da ya sa aka cire shi daga gasar kenan.

Shima Sojon Dogon Jango Guramada ya kai wasan daf da karshe, bayan da Kada daga Kudu ya kasa karasa dambatawar da suke yi.

Za a buga wasannin daf da karshe tsakanin Bahagon Sanin Kurna daga Arewa da Shagon Audu Tunga Guramada, sannan a kece raini tsakanin Ali Kanin Bello daga Arewa da Sojan Dogon Jango Guramada a ranar Asabar.