Liverpool ta lallasa Swansea da ci 2-1

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Liverpool

Kulob din Liverpool ya lallasa Swansea da ci 2-1 a fafatawar da suka yi ranar Asabar din nan a gasar Premier ta kasar Ingila.

Kafin a tafi hutun rabin lokaci dai, Swansea ce ke kan gaba da ci daya.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne dan wasan Liverpool, Roberto Firmino ya rama kwallon a minti na 54.

A minti na 84 kuma James Milner ya kara kwallo ta biyu a bugun daga kai sai mai tsaron gida.