Chelsea ta lallasa Hull City da ci 2-0

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan Chelsea

A fafatawarsu a gasar Premier ta Ingila, kulob din Chelsea ya doke Hull City a filin wasa na KCOM da ci 2-0.

Kulob din Hull City ne dai ya fi yin abin a zo a gani kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma lamarin ya sauya bayan Willian ya zurara musu kwallo ta farko a raga.

Diego Costa ne ya ci wa Chelsea kwallon ta biyu.

Tun bayan zura mata kwallaye biyu a ragarta, kungiyar Hull City ba ta kara yin katabus ba a sauran lokacin wasan.

Dama kocin Chelsea Antonio Conte ya sha alwashin sauya salon taka leda tun bayan kashin da kulob din ya ssha a hannun Arsenal a makon jiya.