Dambe: Kanin Bello da Shagon Audu wasan karshe

Ali Kanin Bello da Shagon Audu Tunga
Bayanan hoto,

Jama'a sun zaku da ganin wannan karon-batta na Ali Kanin Bello da Shagon Audu Tunga

Ali Kanin Bello zai dambata da Shagon Audu Tunga a wasan karshe a damben mota a filin wasa na Ado Bayero Square da ke jihar Kano a ranar Lahadi.

Ali Kanin Bello dan damben Arewa ya kai wasan karshe ne, bayan da ya doke Sojan Dogon Jango Guramada a turmin farko a wasan daf da karshe da suka yi.

Shi kuwa Shagon Audu Tunga Guramada ya kai wasan karshe ne, bayan da ya buge Bahagon Sanin Kurna daga Arewa shi ma a Turmin farko.

Kafin wasan karshen za a buga fafatawar neman mataki na uku da na hudu a tsakanin Bahagon Sanin Kurna da Sojan Dogon Jango.

A karshen gasar wadda aka yi wa lakabi da Mohammad Sunusi na biyu Sarkin Kano, zakara zai lashe mota, na biyu ya karbi babur, sannan a bai wa na uku kudi naira 50,000, yayin da na hudu zai karbi naira 20,000.

Haka kuma za a yi wa wanda ya lashe gasar nadi da kuma ba shi sandar girma.