An kama magoya bayan West Ham Uku

West Ham United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan West Ham United

Jami'an tsaro sun kama magoya bayan West Ham United uku a sabon filin kungiyar, bayan kammala karawar da ta yi da Middlesbrough a ranar Asabar.

West Ham United ce ta karbi bakuncin Middlesbrough a gasar cin kofin Premier, inda suka tashi kunnen doki 1-1.

Jami'an tsaron sun ce sun kama mutane biyu da laifin tada hatsaniya da kuma mutun guda da laifin cin zarafin dan sanda.

Bayan da aka tashi daga karawar sai da jami'an tsaro suka raka magoya bayan Middlesbrough, inda suka ba su kariya daga harin magoya bayan West Ham.

Ana ta samun karin hargitsi a sabon filin wasa na West Ham United mai suna Olympic tun bayan da ta koma can da murza-leda daga Upton Park.

A wasan farko a gasar Premier bana da ta yi da Bournemouth sai da 'yan kallo suka je karawar da tikiti na jabu, daga baya fada ya barke tsakanin magoya bayan kungiyoyin biyu daga wajen filin wasa.