Lalana ba zai yi wa tawagar Ingila wasa ba

Adam Lalana

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Dan kwallon Liverpool, Adam Lalana

Dan kwallon Liverpool, Adam Lalana, ba zai buga wa tawagar kwallon kafa ta Ingila wasanni biyu ba, sakamakon raunin da ya yi.

Lalana ya yi rauni ne a karawar da Liverpool ta doke Swansea 2-1 a gasar cin kofin Premier.

Ingila za ta buga wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da Malta a ranar Asabar a Wembley, sannan ta ziyarci Slovenia a ranar Talata.

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, na fatan nan da mako biyu masu zuwa Lalana zai murmure ya kuma dawo da buga wa kungiyar Tamaula.

Liverpool za ta karbi bakuncin Manchester United a gasar Premier a ranar 17 ga watan Oktoba.