Man United ta buga 1-1 da Stoke City

Asalin hoton, EPA
Kocin Man U Jose Mourinho
Manchester United ta tashi wasa kunnen doki 1-1 da Stoke City a gasar Premier da suka yi a Old Trafford a ranar Lahadi.
United ce ta fara cin kwallon ta hannun Anthony Martial, yayin da Stoke ta farke ta hannun Joe Allen.
Da wannan sakamakon United ta hada maki 13 tana kuma mataki na shida a kan teburin Premier a wasanni bakwai da ta yi.
Ita kuwa Stoke City tana matsayi na 19 da maki uku a wasnni bakwai da ta buga a gasar ta Premier.
United za ta ziyarci Liverpool a wasan mako na takwas a ranar Litinin 17 ga watan Oktoba.