Tottenham ta ci Man City 2-0

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Tottenham Dele Alli ya zura kwallo ta biyu
Tottenham ta doke Manchester City da ci 2-0 a gasar Premier wasan mako na bakwai da suka kara a White Hart Lane a ranar Lahadi.
City ce ta fara cin gida ta hannun Aleksandra Kolorov a minti na tara da fara wasa.
Tottenham ta ci kwallon na biyu ne ta hannun Dele Alli saura minti takwas a je hutun rabin lokaci.
Tottenham ta takawa City burki a yawan lashe wasannin Premier bayan da ta ci shida a jere karkashin Pep Guardiola wanda ya fara jan ragamar kungiyar a kakar bana.
Manchester City ta ci gaba da zama a matsayi na daya a kan teburi da maki 18, yayin da Tottenham ke mataki na biyu da maki 17.