Dambe: Shagon Audu Tunga ya ci mota

dambe, kano, Shagon Audu Tunga
Bayanan hoto,

Makashin maza Shagon Audu Tunga

Shagon Audu Tunga ya lashe mota a gasar damben gargajiya ta mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu da aka yi wasan karshe a ranar Lahadi.

Shagon Audu Tunga Guramada ya samu nasarar doke Ali kanin Bello daga Arewa kasa da minti daya a karon-battar da suka yi a gidan dambe na Ado Bayero Square da ke Kano.

Bahagon Sanin Kurna daga Arewa ne ya yi na uku a gasar bayan da ya doke Sojan Dogon Jango Guramada.

Alhaji Muhammad Aliyu, Dogacin Kano, Hakimin Garko shi ne ya wakilci Sarkin Kano, Inda ya bai wa Audu Tunga Kofi da kuma makullin motar.

Haka kuma an nada zakaran gasar, Shagon Audu Tungan a matsayin Sarkin Damben gargajiya na jihar Kano.