Song ya farfado daga suman kwana biyu da ya yi

Tawaga
Bayanan hoto,

Tsohon dan kwallon tawagar Kamaru

Tsohon dan wasan tawagar kwallon kafa ta Kamaru, Rigobert Song, ya farfado daga suman kwana biyu da ya yi, za kuma a kaishi Faransa yin magani.

A ranar Lahadi aka kai Song mai shekara 40 babban asibitin Yaounde bayan da ya fadi magashiyan.

Dakta Louis Joss Bitang A Mafok, daraktan babban asibitin Yaounde ya ce tuni aka cire masa abin da ke taimaka masa nunfashi.

Likita Mafok ya kara da cewar za a kai Song Faransa domin a duba lafiyarsa.

Song ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Kamaru wasanni 137, ya kuma taka leda a Liverpool da West Ham United.

Yanzu haka yana aiki a matsayin kociyan hukumar kwallon kafa ta Kamaru, bayan da ya bar aikin horar da Chadi.