Ina son a kara kasashen da ke buga kofin duniya — Infantino

Fifa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A ranar 26 ga watan Fabrairu aka zabi Infantino a matsayin shugaban hukumar Fifa

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, Gianni Infantino, ya mika aniyar fadada gasar cin kofin duniya zuwa kasashe 48 da za su yi gumurzu a wasanni.

Tun farko shugaban ya bayar da shawarar cewa a kara kasashe hudu a kan 36 da suke buga gasar, yanzu kuma ya bukaci da su koma 48.

Infantino ya ce za a fitar da kasashe 16 a wasannin share fage a gasar cin kofin duniya a sabon tsarin, daga nan kuma a raba sauran 32 zuwa rukuni kamar yadda aka saba.

Shugaban ya ce watakila a yanke hukuncin komawa sabon tsarin fadada gasar cin kofin duniyar a cikin watan Janairu.

A cikin watan Fabrairu aka zabi Infantino a matsayin sabon shugaban hukumar ta Fifa, inda ya maye gurbin Sepp Blatter.

Daya daga cikin alkawarin da ya yi a lokacin kamfen dinsa shi ne kara kasashe hudu kan 36 da suke buga gasar kofin duniya.