Bruce zai dace ya horar da Aston Villa - Savage

Asalin hoton, Rex Features
Bruce ya bar horar da Birmingham a shekarar 2007, inda ya koma jan ragamar Wigan
Robbie Savage ya ce Steve Bruce zai dace ya jagoranci Aston Villa domin maye gurbin Roberto di Matteo.
Rabon da Bruce ya horar da wata kungiya tun a cikin watan Yuni, bayan da ya bar Hull City.
Aston Villa ta kori Roberto di Matteo ne a ranar Litinin.
Savage ya ce Bruce yana da kwarewar da ta dace, sannan kuma yana zaune a yankin da kungiyar take, ya kara da cewar shi ne ya daga Birmingham da Hull City a fagen tamaula.
Bruce ya fara jan ragamar Birmingham a shekarar 2001, ya kuma kai su gasar Premier a 2002.