Fifa ta dau mataki kan kasashe 11

Fifa
Bayanan hoto,

Fifa ta dauki matakin ladabtarwa sakamakon laifin da magoya bayan kasashen suka aikata

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta dauki matakin ladabtarwa a kan hukumomin kwallon kafa 11, saboda nuna halin rashin da'a da cin zarafi da magoya bayansu suka yi.

Kasashen sun hada da Honduras, El Salvador, Mexico, Canada, Chile, Brazil, Argentina, Paraguay, Peru, Italy da Albania wadan aka ci tarar su kudi.

Magoya bayan kasashen sun nuna halin rashin kyautawar ne a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya ta 2018.

Fifa ta umarci Chile da ta buga wasan da za ta yi da Venezuela babu 'yan kallo da za su kara a ranar 28 ga watan Maris a shekarar 2017.

Tarar kudin ta fara daga fam 52,009 da aka ci Honduras kan laifuka guda biyu da magoya bayanta suka yi sau biyu zuwa fam 16,002 da Brazil da Canada za su biya.