'Yan wasan Madrid 15 ne za su yi wa kasashensu wasa

Porugal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ronaldo zai buga wa Portugal karawar da za ta yi da Andorra a ranar Juma'a

Kimanin 'yan wasan Real Madrid 15 ne aka gayyata cikin tawagar kasashensu, domin buga wasannin shiga gasar kofin duniya ko buga wasan sada zumunta ko na matasa.

Tun a ranar Alhamis da kuma karshen makonnan za a ci gaba da buga wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya ta 2018.

'Yan wasan Madrid da za su buga wasannin shiga gasar cin kofin duniya sun hada da Carvajal, Sergio Ramos, Nacho, Isco, Lucas Vázquez, Morata, Cristiano Ronaldo, Pepe, Varane, Kroos, Kovacic, Bale da kuma James.

Shi kuwa Keylor Navas zai buga wasan sada zumunta ne da Costa Rica za ta kara da Rasha a Krasnodar a ranar Litinin

Asensio zai yi wa Spaniya wasan da za ta yi da Estoniya a neman gurbin shiga gasar matasa 'yan shekara 21 a ranar Litinin.