Za a soke lasisin Fury dan damben boksin

Fury

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tyson Fury ne ya sanar da cewar yana amfani da hodar Ibilis

Watakila hukumar wasan damben boksin ta duniya ta kwace lasisin Tyson Fury, bayan da dan wasan ya ce yana amfani da hodar Ibilis.

Fury dan Birtaniya, mai shekara 28, wanda ya ce ya yi ritaya daga wasan a ranar Litinin, ya kuma ce yana fama da damuwa.

Sakatare Janar na hukumar tsabtace wasan damben boksin ta Birtaniya, Robert Smith, ya ce amfani da hodar Ibilis laifi ne.

A ranar 12 ga watan Oktoba hukumar za ta yi taro kan batun, ta taba soke lasisin Ricky Hatton bayan da aka zargi dan damben da shan abubuwa masu kara kuzari.