Murray da Edmund za su kara a China Open

Murray

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Murray ya doke Edmund a haduwar da suka yi a 2015

Andy Murray ya kai wasan daf dana kusa da na karshe a gasar kwallon tennis ta China Open, bayan da ya doke Andrey Kuznetsov.

Murray y samu nasara ne da ci 6-2, 6-1 a fafatawar da suka yi awa daya da minti 16 a Beijing.

Da wannan sakamakon Murray dan Birtaniya zai kara da Kyle Edmund shi ma dan Birtaniyan a wasan daf da na kusa da na karshe.

Edmund ya kai wasan gaba ne, bayan da ya doke Roberto Bautista da ci 6-4 4-6 6-4.

Murray da Edmund sun taba karawa sau daya a gasar da aka yi Queens a shekarar 2015.