Italiya za ta karbi bakuncin Spaniya

Italy

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Italia za ta karbi bakuncin Spaniya a ranar Alhamis

Tawagar kwallon kafa ta Spaniya za ta ziyarci ta Italiya, domin buga wasan shiga gasar cin kofin duniya da za su buga a ranar Alhamis.

Kasashen biyu sun kara a manyan wasannin tamaula a tsakaninsu sau 35, Italiya ta samu nasara sau 11, yayin da Spaniya ta ci karawa 10 suka yi canjaras a fafatawa 14.

Spaniya wadda ke mataki na 11 a jerin kasashen da suke kan gaba wajen taka leda a duniya da Italiya wadda ke matsayi na 13, suna rukuni daya da Albaniya da Macedonia da Isra'ila da kuma Liechtenstein.

Haka kuma Italiya da Spaniya da Albaniya suna da maki biyu-biyu a rukuni na bakwai, inda sauran kasashen basu da maki ko daya daga wasannin farko a rukuni da suka yi.