Kofin duniya: Brazil za ta kara da Boliva

Brazil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Brazil tana mataki na biyu a kan teburin shiyyar Kudancin Amurka

Tawagar kwallon kafa ta Brazil za ta karbi bakuncin ta Bolivia a wasan shiga gasar cin kofin duniya a shiyyar Kudancin Amurka a ranar Juma'a.

Brazil tana mataki na biyu a kan teburi da maki 15 a wasanni takwas da ta buga, yayin da Bolivia ke matsayi na takwas da maki bakwai.

Ita kuwa tawagar kwallon kafa ta Argentina za ta ziyarci ta Peru a ranar ta Juma'a a wasan shiga gasar cin kofin duniya.

A makon nan hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta dauki matakin ladabtarwa a kan hukumomin kwallon kafa 11, saboda nuna halin rashin da'a da cin zarafi da magoya bayansu suka yi.

Kasashen sun hada da Honduras, El Salvador, Mexico, Canada, Chile, Brazil, Argentina, Paraguay, Peru, Italy da Albania wadan aka ci tarar su kudi.

Tarar kudin ta fara daga fam 52,009 da aka ci Honduras kan laifuka guda biyu da magoya bayanta suka yi sau biyu zuwa fam 16,002 da Brazil da Canada za su biya.