Iniesta ya cika shekara 20 a Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Iniesta ya fara buga wasa a Barcelona a ranar 6 ga watan Oktoban 1996
Andres Iniesta ya cika shekara 20 tare da Barcelona, bayan da ya fara yi wa matasan kungiyar masu shekara kasa da 14 wasanni, kwanaki 20 da ya je can.
Iniesta ya je Barcelona a ranar 6 ga watan Oktoba a 1996, ya kuma fara buga wa babbar kungiyar tamaula a ranar 29 ga watan Oktoban 2002, yana da shekara 18.
Dan wasan wanda aka haifa a ranar 11 ga watan Mayun 1984 a Fuentealbilla a Spaniya ya fara wasa a Albacete a shekarar 1994 zuwa 1996 daga nan ya koma karamar kungiyar Barcelona.
Iniesta ya buga wa Barcelona wasanni 654 jumulla ya kuma ci mata kwallaye 60.
Ga jerin kofunan da ya lashe a Barcelona.
- La Liga 8: 2004-05, 2005-06, 2008-09, 2009-10, 2010-11, 2012-13, 2014-15, 2015-16
- Copa del Rey 4: 2008-09, 2011-12, 2014-15, 2015-16
- Supercopa de España 7: 2005, 2006, 2009, 2010, 2011, 2013, 2016
- UEFA Champions League 4: 2005-06, 2008-09, 2010-11, 2014-15
- UEFA Super Cup 3: 2009, 2011, 2015
- FIFA Club World Cup 3: 2009, 2011, 2015