Matasan Ingila sun samu gurbin gasar nahiyar Turai

Leicester

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Demarai Gray yana cikin 'yan wasan Leicester City da suka lashe kofin Premier a bara

Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta matasa 'yan kasa da shekara 21, sun samu gurbin buga gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan da ta ci ta Kazakhstan 1-0.

Demarai Gray ne ya ci wa Ingila kwallon, wanda ya sa ta samu tikitin shiga gasar ta matasan da za a yi a 2017 a cikin watan Yuni a Poland, duk da saura wasa daya ya rage.

Gareth Southgate ne ya jagoranci matasan tun farko, wanda daga baya ya karbi aikin horar da babbar tawagar Ingila, bayan da aka kori Sam Allardyce.

Aidy Boothroyd ne ya maye gurbin Southgate a matsayin kociyan rikon kwarya.

Tawagar matasan Ingila za ta buga wasan karshe da ta Bosnia da Herzegovina a Walsall a ranar Talata 11 ga watan Oktoba.