Italiya da Spaniya sun tashi kunnen doki 1-1

Spain

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

De Rossi ne ya farke kwallon da Spaniya ta ci su a bugun fenariti

Italiya da Spaniya sun buga kunnen doki 1-1 a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka buga a ranar Alhamis.

Spaniya ce ta fi taka rawa a minti na 45 da fara tamaula, amma kwallo ta kasa shiga raga har sai da aka dawo daga hutu ne Machín Pérez ya ci mata kwallo.

Saura minti takwas a tashi daga fafatawar Italiya ta farke ta hannun De Rossi a bugun fenariti.

Albania ce ta daya a rukuni na bakwai da maki shida a wasanni biyu-biyu da suka buga, sai Spaniya da Italida da suke da maki hudu kowannensu.