Southgate ya fara horar da Ingila da nasara

England

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Southgate zai ja ragamar Ingila a wasanni hudu a matsayin kociyan rikon kwarya

Kociyan rikon kwarya na Ingila, Gareth Southgate, ya fara jan ragamar tawagar kwallon kafar kasar da kafar dama, bayan da ya samu nasara a kan Malta da ci 2-0.

Kasashen biyu sun kara ne a Wembley a ranar Asabar a wasan shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Ingila ce tafi taka rawa a karawar, inda mai tsaron ragar Malta, Andrew Hogg, ya hana kwallon da Wayne Rooney ya buga ta shiga raga da wadda Dele Ali ya sa kai.

Daga baya ne Daniel Sturridge da kuma Dele Alli suka ci wa Ingila kwallo.

Southgate ya karbi aikin kociyan Ingila, bayan da hukumar kwallon kafar kasar ta raba gari da Sam Allardyce.