Gabon da Morocco sun tashi wasa canjaras 0-0

Morocco

Asalin hoton, Carl de Souza/Getty

Bayanan hoto,

Pierre-Emerick Aubameyang ya yi kokarin ganin tawagar kwallon kafa ta Gabon ta doke ta Morocco

Gabon da Morocco sun tashi canjaras 0-0 a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka buga a Franceville a ranar Asabar.

Gabon wadda za ta karbi bakuncin gasar kofin Afirka a 2017 ta yi ta kokarin ganin ta ci kwallo domin ta taka rawar gani a wasannin.

Rabon da Morocco wadda Herve Renard ke jagoranta ta je gasar cin kofin duniya tun wadda aka yi a Faransa a 1998.

Ita kuwa Gabon bata taba zuwa gasar cin kofin duniya ba a tarihi.