Super Eagles za ta kara da tawagar Zambia

Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Karo biyu a jere Super Eagles ta kasa samun tikitin buga gasar kofin nahiyar Afirka

Tawagar kwallon kafa ta Zambia ta karbi bakuncin ta Nigeria, domin buga wasan shiga gasar cin kofin duniya da za su kara a ranar Lahadi.

Super Eagles karkashin jagorancin ministan matasa da wasanni, Barrista Solomom Dalung, ta sauka a Zambia a ranar Asabar.

Kasashen biyu za su fafata ne a Ndola a wasan farko na cikin rukuni na biyu da ya kunshi Kamaru da Algeria.

A kuma ranar Lahadin tawagar kwallon kafa ta Algeria za ta karbi bakuncin ta Kamaru.

Kasa daya ce za ta wakilci Afirka a wannan rukunin daga cikin guda biyar da za su wakilceta a gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.