Super Eagles ta ci Zambia 2-1

Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Nigeria ta taba doke Zambia 2-1 a shekarar 1994 a gasar kofin Afirka

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta doke ta Zambia da ci 2-1 a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da suka kara a Ndola a ranar Lahadi.

Nigeria ce ta fara cin kwallo ta hannun Alex Iwobi a minti na 35 da taka-leda, sannan ta ci ta biyu ta hannun Kelechi Iheanacho saura minti uku a tafi hutun rabin lokaci.

Zambia ta samu damar zare kwallo daya ta hannun Collins Mbesuma, bayan da mai tsaron baya na Super Eagles, Keneth Omeruo ya yi sakaci.

Nigeria ta taba cin Zambia 2-1 a wasan karshe na cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 1994.

Super Eagles za ta karbi bakuncin Algeria a wasa na biyu na cikin rukuni na biyu a ranar 6 ga watan Nuwamba, a ranar kuma Kamaru da Zambia za su kece raini.