Dambe: Mai Takwasara da na Mai Maciji babu kisa

Turmi biyu suka taka aka raba su a karawar da suka yi a Dei-Dei da ke Abuja, Nigeria
Bahagon Mai Maciji da Mai Takwasara sun tashi damben babu kisa a karawar da suka yi a ranar Lahadi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria.
Bahagon Mai Maciji dan damben Kudu shi ne ya taro Mai Takwasara Guramada, inda suka yi turmi biyu babu kisa aka raba su.
Tun kafin nan Shagon Dan Digiri ne daga Kudu ya buge Shagon Shikurana daga Arewa a turmin farko.
Shi ma Aminu Shagon Langa-Langa daga Arewa doke Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu ya yi a turmin farko.
Sai dai kuma sa zare da aka yi tsakanin Dogon Kyallu Guramada da Shagon Aleka daga Kudu turmi daya kacal suka taka aka kuma raba su aka tashi daga wasan.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti Daya da BBC Safe 23/01/2021, Tsawon lokaci 1,13
Minti Ɗaya Da BBC na Safiyar 23/01/2021, wanda Nabeela Mukhtar Uba da Sani Aliyu su ka karanto.