Tennis: Murray ya lashe gasar China Open

Tennis
Bayanan hoto,

Sau tara Andy Murray ya buga wasannin karshe a gasar kwallon tennis a shekarar 2016, inda ya ci karawa biyar

Andy Murray ya lashe gasar kwallon tennis ta China Open, bayan da ya samu nasara a kan Grigor Dimitrov da ci 6-4 7-6 (7-2).

Wannan kuma shi ne kofi na biyar da ya ci a shekarar 2016, sannan kuma na 40 a matsayin dan wasa daya a gasar kwallon tennis.

A wasan mata kuwa a gasar tennis ta Chine Open da aka kammala, Agnieszka Radwanska ce ta lashe kofin.

Radwanska ta samu nasarar doke Johanna Konta da ci 6-4 6-2.