Tennis: Edmund zai kara da Wawrinka

Tennis

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wawrinka na fatan ya taka rawar gani a gasar Shanghai

Kyle Edmund zai fafata da Stan Wawrinka a wasan zagaye na biyu a gasar kwallon tennis ta Shanghai Masters.

Edmund dan Birtaniya ya kai wasan zagaye na biyu ne, bayan da ya doke Federico Delbonis dan Argentina da ci 6-3 5-7 6-4.

A makon jiya Edmund ya yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Andy Murray a gasar kwallon tennis ta China Open.

Wawrinka mai shekara 31, na fatan lashe kofi na biyar a shekarar 2016, a gasar da ake yi ta Shanghai.