Rooney zai zauna a benci a ranar Talata

England

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Wayne Rooney kyaftin din Manchester United

Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Ingila, Wayne Rooney zai zauna a benci a wasan neman shiga gasar kofin duniya da kasar za ta yi da Slovenia a ranar Talata.

Kociyan rikon kwarya na tawagar Ingila, Gareth Southgate, zai ajiye Rooney ne, bayan da dan wasan ya buga fafatawar da kasar ta ci Malta 2-0 a ranar Asabar.

Rooney shi ne dan wasan Ingila da ya fi yawan buga wa tawagar kwallon kafar wasanni, inda ya buga mata tamaula sau 117.

Sai dai kuma a ranar Asabar wasu magoya bayan kasar sun yi wa Rooney ihu a karawar da Ingila ta ci Malta a Wembley.

Southgate ya ce bai kamata a yi wa kyaftin din Ingila haka ba, domin ya taka rawar gani a tawagar kwallon kafar kasar, kuma irin wannan hali zai sanyaya gwiwar 'yan baya.