Ko Nigeria za ta iya shiga gasar kofin duniya a 2018?

  • Muhammad Abdu
  • BBC Hausa, Abuja
Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rabon da Nigeria ta ci wasa a waje tun bayan da ta doke Congo 2-1 a 2015

A ranar Lahadi Super Eagles ta ci tawagar kwallon kafa ta Zambia 2-1 a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka kara a Ndola.

Wasan wanda shi ne na farko a rukuni na biyu, ya sa Nigeria tana mataki na daya a kan teburi, bayan da Algeria da Kamaru suka tashi kunnen doki a ranar ta Lahadin.

Nigeria ta samu nasara a Zambia duk da isa kasar da ta yi a makare, bayan da shugaban hukumar kwallon kafa ta Nigeria Amanju Pinnick ya c e ba su da kudin da za su je wasan.

Rabon da Super Eagles ta ci wasa a waje tun a 2015, bayan da ta doke Congo 2-1 a wasan shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka a Pointe Noire.

A shekarar 2017 za a buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a fafata a Gabon, sai dai Super Eagles ba za ta buga wasannin ba, kuma karo na biyu kenan a jere, bayan da kasar ta kasa shiga gasar da aka yi a 2015.

Bayanan hoto,

Kociyan ya ci wasanni biyu kenan tun da ya karbi aiki a cikin watan Agusta

Nasarar da Nigeria ta yi a Zambia ta karawa 'yan kasar kwarin gwiwa, bayan da sabon kociya Gernot Rohr da sabbin 'yan wasan da ya gayyata suka nuna cewar da gaske suke.

Super Eagles wadda ke mataki na 14 a iya murza-leda a Afirka, za ta buga wasan gaba da Algeria wadda ke matsayi na biyu a ranar 12 ga watan Nuwamba a Uyo.

A cikin runkunin na biyu, za a zabi kasa daya da ta fi yawan maki domin wakiltar Afirka daga cikin guda biyar din da za su wakilceta a gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Nigeria ta je wasannin cin kofin duniya sau biyar tun daga shekarar 1994 da 1998 da 2002 da 2010 da kuma 2014.