Pique zai yi ritayar buga wa Spaniya tamaula

Spain

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Pique mai taka leda a Barcelona ya ce ya gaji da yadda magoya bayan Spaniya ke yin cece-kuce a kansa

Mai tsaron baya Gerard Pique zai yi ritaya daga buga wa tawagar kwallon kafa ta Spaniya tamaula, bayan kammala Gasar cin Kofin Duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Pique, mai shekara 29, ya yi bakin-jini a wajen magoya bayan Spaniya, bayan da ya goyi bayan a bai wa Catalonia 'yancin cin gashin kai.

Dan kwallon ya sha suka bayan da Spaniya ta ci Albania 2-0, sai dai kuma a hannun rigarsa babu bajon kasar kamar yadda sauran 'yan wasan suke da shi.

Hukumar kwallon kafa ta Spaniya ta kare dan wasan inda ta ce rigar da ya saka mai dogon hannu ce, irin wadda Sergio Ramos ya saka, wadanda ba su da bajon Spaniya.

Ta kuma kara da cewar Pique ne ya yanke dogon hannun zuwa gajere kamar yadda wasu 'yan wasa ke yi idan an zo buga tamaula.

Pique, wanda ya ci Kofin Duniya a 2010 da na Zakarun Turai na 2012 da Spaniya, ya ce ya yi wa kasar iya kokarinsa, ba zai jure wulakanci ba.