Sergio Ramos zai yi jinyar wata daya

Spaniya

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Ramos shi ne dan kwallo na biyu da ya fi yawan buga wa tawagar Spaniya wasanni, inda ya buga mata tamaula sau 139

Dan wasan Real Madrid Sergio Ramos ya yi rauni a gwiwarsa a karawar da Spaniya ta doke Albania a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka fafata a ranar Lahadi.

An sauya Ramos, mai shekara 30, daga wasan saura minti 10 a tashi daga karawar a lokacin da kafarsa ta yi tsami.

Dan kwallon mai tsaron baya zai yi jinyar wata daya, hakan kuma zai sa ba zai buga wasannin La Liga hudu ba, ciki har da karawar da Real Madrid za ta yi da Atletico.

Haka kuma Ramos ba zai buga wa Real Madrid gasar cin kofin zakarun Turai da za ta buga da Legio Warsaw da kuma karawar da Spaniya za ta yi da Macedonia a ranar 12 ga watan Satumba ba.