Super Falcons ta gayyaci 'yan wasa 30

Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Nigeria ta lashe kofin nahiyar Afirka sau tara

Mai horar da tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria, Florence Omagbemi, ta gayyaci 'yan wasa 30 domin fara shirin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta bana.

Cikin 'yan wasan da ta gayyata guda 22 masu taka-leda ne a cikin gida, yayin da sauran su ke murza-leda a kasar waje ne.

Za a buga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata a Kamaru daga ranar 19 ga watan Nuwamba zuwa 3 ga watan Disambar 2016.

Ga jerin 'yan wasan da aka gayyata:

'Yan wasan da suke taka-leda a gida: Ibubeleye Whyte, Osinachi Ohale, Gladys Akpa, Ugo Njoku, Chioma Wogu, Glory Iroka (Rivers Angels); Blessing Edoho (Pelican Stars); Osarenoma Igbinovia, Alaba Jonathan (Bayelsa United); Nkemakola Uwandu (Inneh Queens); Rita Akarekor, Alice Ogodo (Delta Queens); Seun Bello, Maureen Toyla (Confluence Queens); Nnenna Eke (Ibom Angels); Gladys Abasi, Sherifat Saheed, Yetunde Aluko, Ijeoma Obi (Sunshine Queens); Anam Imo (Nasarawa Amazons); Nnenna Julius, Chioma Nwankwo (Adamawa Queens)

Masu taka-leda a waje: Rita Chikwelu (Umea IK, Sweden); Ngozi Okobi (Vittsjo FC, Sweden); Faith Ikidi (Pitea IF, Sweden); Ngozi Ebere (PSG Ladies, France); Evelyn Nwabuoku (Avant Guingamp, France); Desire Oparanozie (Avant Guingamp, France); Francisca Ordega (Washington Spirit, USA); Asisat Oshoala (Arsenal Ladies)