Madrid ta yi wasanni 19 ba a doke ta ba

La Liga
Bayanan hoto,

Real Madrid ce ke rike da kofin zakarun Turai na bara da ta lashe

Real Madrid ta yi wasanni 19 a jere a gasar La Liga ba tare da ta yi rashin nasara ba, guda 12 tun a kakar da ta wuce da wasanni bakwai a fafatawar bana.

Madrid din ta ci wasanni 16 ta yi canjaras a karawa uku jumulla, sannan ta ci kwallaye 55 an kuma zura mata 16 a raga.

Bayern Munich ce ta biyu wadda ta buga wasanni 16 a jere ba a doke ta ba a gasar Bundeslida sai Cologne da ta yi wasanni 11.

A gasar Faransa Nice ta yi karawa 10 ba ta yi rashin nasara ba, sai Atletico Madrid da ta buga wasanni takwas a gasar La Liga ba a ci ta ba.