Za a dawo da gasar kwallon kafa a Saliyo

Karon farko da aka ci kofin kwallon kafa a Saliyo tun bayan da aka dakatar da buga tamaula a kasar don kaucewa yada cutar Ebola
Hukumar kwallon kafa ta Saliyo na fatan ci gaba da gasar kasar a karon farko, tun bayan da aka dakatar da wasannin sakamakon bullar cutar Ebola.
Tun a kakar wasan 2014 hukumar kwallon kafa ta Saliyo ta dakatar da buga wasannin kasar domin kauncewa yada cutar ta Ebola.
A cikin watan Maris hukumar lafiya ta duniya ta wanke Saliyo daga cikin kasashen da suke da cutar ta Ebola.
A ranar Asabar aka buga wasan karshe na cin kofin kalubalen kasar, wanda hakan ya sa ake ta kiraye-kirayen cewar a dawo da gasar Premier kasar.
A wasan karshen FC Johansen ce ta doke Republic of Saliyo Armed Forces.