Bryant ya yi gwanjon abin kare fuskarsa

Asalin hoton, Getty Images
Kobe ne dan wasan kwallon kwandon da ya yi shekara 20 a kungiya daya
Tsohon dan wasan kwallon kwando, Kobe Bryant, ya yi gwanjon abin da ke kare masa fuska domin tara kudin da zai taimaka wa gajiyayyu.
Braynt ya yi amfani da abin kare fuskar ne a wasannin da ya yi wa kungiyar Los Angeles Lakers, an kuma fara taya abin kan kudi dala 15,000.
Dan wasan ya yi amfani ne da abin kariyar bayan da ya yi rauni a karan hanci a shekarar 2012.
A baya, dan wasan kwallon kwandon ya yi gwanjon abin kariyar fuska da ya yi amfani da shi a 2012, wanda aka saya dala 67,000 kuma ya saka kudin a gidauniyar iyalan Kobe da Vanessa.