Jamus ta doke Ireland ta Arewa da ci 2-0

Germany

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jamus ce ta daya a kan teburi a rukuni na uku

Tawagar kwallon kafa ta Jamus ta doke ta Ireland ta Arewa da ci 2-0 a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka kara a ranar Talata.

Julian Draxler ne ya fara cin kwallo a minti na 13 da fara tamaula, sannan Sami Khedira ya ci ta biyu minti hudu tsakani.

A gasar cin kofin nahiyar Turai da aka yi a Faransa a bana, Jamus ce ta doke Ireland ta Arewa da ci daya mai ban haushi.

Jamus ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da maki tara, sai Azerbaijan ta biyu da maki bakwai, yayin da Ireland ta Arewa ta hada maki hudu a matsayi na uku.

Norway maki uku ne da ita sai Jamhuriyar Czech mai maki biyu da San Marino wadda ba ta da maki ko daya.