An yi korafi kan alkalin wasan United da Liverpool

An haifi Anthony Taylor a Wythenshawe mil shida tsakaninsa da filin Manchester United
Tsohon shugaban hukumar alkalan wasa ta Ingila, Keith Hackett, ya yi korafi kan nada Anthony Taylor a matsayin wanda zai yi alkalancin wasan da za a yi tsakanin Manchester United da Liverpool.
A ranar Litinin Liverpool za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan Premier da za su kara a Anfield.
Hackett ya ce gidan da Taylor ke zama yana mil shida tsakaninsa da filin Old Trafford, wanda hakan zai iya kawo zargin magudi a karawar.
Ya kuma kara da cewar babu wanda zai ce Taylor ba shi da kwarewa, amma duk wani zargi da zai taso idan aka samu matsala, yana da tushe.
Taylor bai taba hada sabga da United ba, hasalima kungiyar Altrincham yake marawa baya, wadda take buga National League a Kudancin kasar.