Kross ya sabunta kwantiraginsa a Madrid

Spain

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kross dan wasan tawagar kwallon kafa ta Jamus zai ci gaba da murza-leda a Madrid

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Jamus, Toni Kross, ya sabunta yarjejeniyarsa da Real Madrid domin ci gaba da buga mata tamaula zuwa 2022.

Dan kwallon mai shekara 26, wanda ya koma Bernabeu daga Bayern Munich a shekara 2014, ya ci wa Madrid kwallaye hudu a wasanni 108 da ya buga mata.

A watan Satumba aka yi ta rade-radin cewar dan kwallon zai koma Manchester United da taka-leda, domin maye gurbin Paul Scholes.

Mujallun Spniya sun wallafa cewar Kross zai dunga karbar fam 346,000 a kowanne mako.