An yaba wa Aurier kan ceton rai da ya yi

Mali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ivory Coast ce ta lashe karawar da ta yi da Mali a ranar Asabar

An yaba wa dan kwallon Paris Saint-Germain, Serge Aurier, kan ceto ran Moussa Doumbia dan wasan tawagar Mali da ya yi a ranar Asabar.

Doumbia ya fadi kasa a lokacin da ya yi karo da Lamine Kone a wasan shiga gasar cin kofin duniya da Mali ta ziyarci Ivory Coast.

Dan kwallon na faduwa kasa sai ya yi kokarin tauna harshensa, a lokacin ne Aurier ya yi sauri ya bude bakin Doumbia har sai da ya farfado.

Bayan kammala karawar kociyan Mali, Alain Giresse ya yi magana da Aurier ya kuma gode masa kan ceton ran da ya yi.

Daga karshe Ivory Coast ce ta lashe wasan da ci 3-1 a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka fafata a Bouake.