Rajevac ya bar aikin horar da Algeria

Algeria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Milovan Rajevac shi ne ya horar da Ghana har kasar ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a kofin duniya a 2010

Milovan Rajevac ya yi murabus daga aikin horar da tawagar kwallon kafa ta Algeria, bayan da ya jagoranci kasar wasanni biyu kacal.

Rajevac ya ajiye aikin ne, bayan da Algeria ta buga kunnen doki 1-1 da Kamaru a ranar Lahadi a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka kara.

Kociyan mai shekara 62, ya tattauna da shugaban hukumar kwallon kafa ta Algeria, Mohamed Raouraoua, a ranar Talata daga baya hukumar ta sanar da ritayar kociyan.

Rajevac ya maye gurbin Christian Gourcuff, dan kasar Faransa, wanda ya bar jan ragamar Algeria a watan Afirilu.

Algeria za ta ziyarci Nigeria a wasan shiga gasar kofin duniya a ranar 12 ga watan Nuwamba.

Kasa daya ce za ta wakilci Afirka a rukuni na biyu da ya kunshi Zambia da Algeria da Kamaru da Nigeria a gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.