UEFA ta ki amince wa da karar da Legia ta shigar

Spain

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An hana 'yan kallo shiga wasan sabo da gudun hatsaniya

Hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa, ta ki amincewa da daukaka karar da Legia Warsaw ta shigar kan karbar bakuncin Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai ba tare da magoya bayanta ba.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da hukumar kwallon kafa ta Turai ta yanke, bayan da magoya bayan kungiyar suka tayar da hatsaniya.

Mogoya bayan Legia sun tayar da rikici a karawar da Borussia Dortmund ta casa kungiyarsu 6-0 a wasan farko na cikin rukuni da suka yi a gasar.

Kungiyar wadda ta buga wasanni biyu a rukuni na shida ba tare da maki ba, an ci tarar ta kudi fam 69,000.

Warsaw za ta fara ziyartar Madrid a ranar 18 ga watan Oktoba, sanan ta karbi bakuncin wasa na biyu a ranar 2 ga watan Nuwamba.